|
MAJALISAR PAPAROMA TA
TATTAUNAWA TSAKANIN MABIYA ADDINAI
Kirista da
Musulmi:
hadin gwiwa
wajen
kawar da
tashin
hankali
tsakanin
mabiya
addinai
daban
daban
SAKON KARSHEN
AZUMIN WATAN RAMALANA,
‘Id al-Fitr 1431
H. / 2010 A.D.
FADAR PAPA ROMA
Ya Ku Yan’ uwa Musulmi,
1 Sallar Id Al Fitr, da take kawo karshen
Azumin Watan Ramalana ta sake ba mu wata dama da za mu sake isar
da fatan alherin mu a madadin Majalisar Paparoma ta Tattauna
Tsakanin Mabiya Addinai tare da taya murna.
A duk cikin wannan watan kun dage kun
sadaukar da kawunanku cikin yin salloli, Azumi, Taimakon
mabukata da karfafa dankon zumuncin iyali da abota. Ko shakka
babu, Allah ba zai kasa yin sakayyar alheri bisa wadannan
kyawawan ayyuka ba.
2 Ina farin cikin lura da cewa mabiya wassu
addinai, masamman ma Kirista suna kusanci Musulmi a wadannan
ranaku kamar yadda ya tabbata wajen aukuwar tarurukan sada
zumunci da ke haifar da musayar da kan danganci addini. Abun
farinciki gare ni da nake kyautata zaton cewa shi ma
wannan sakon zai zamanto wata kyakyawar gudumawa bisa naku
tunanin.
3 Taken da Majalisar Paparoma ta gabatar a
bana, Kirista da Musulmi: hadin gwiwa wajen kawar da tashin
hankali tsakanin mabiya addinai daban daban abu ne da ba
kamar yadda muka so ya zamo ba, yanzu ya zamo wani babban abun
damuwa akalla a wassu yankunan duniya. Ita ma Majalisar Hadin
Gwiwan Tattauna Tsakanin Adinnai Masu Litttafai, wanan taken ta
zaba a matsayin batun nazari, tunani da musayar ra'ayi a taronta
na shekara shekara da a ka yi a birnin Alkahira (23-24 ga
Fabrairu 2010). Bari in bayyana wassu daga cikin shawarwarin da
aka zartar a karshen taron.
4 Abubuwan da suke haddasa tashin hankali
tsakanin mabiya addinai daban daban sun hada da: yin amfani da
addini don biyan bukatun siyasa ko wata manufa daban; Nuna
bambanci na kabilanci ko addini, rabe raben matsayin rayuwa suna
da nasaba ta kai tsaye ko ta wani gefen daban da tashe tashen
hankula tsakanin mabiya addinai. Fatana a nan shi ne Allah ya sa
shugabanni su tsaya tsayin daka wajen kare doka da oda tare da
tabbatar da adalci, da gaskiya don hana 'yan tada zaune tsaye
masu kunna wutar fitina samun damar yin haka.
5 Har ila yau, akwai wassu muhimman
shawarwarai da aka gabatar a taron da muka ambata wadanda suka
hada da: Bude zukatan mu don yafewa juna da sasantawa don zaman
lafiya na amfanin juna, da kuma fahimtar abubuwan da suka hada
mu gami da mutunta daraja da 'yancin kowanne dan adam, ba tare
da wata kyama ta kabilanci ko addini ba, da kuma bukatar
shimfida dokoki a bisa adalci da za su tabbatar da daidaiton
kowa da kowa da kuma jawo hankali kan muhimmancin ilimantarwa
bisa mutuntawa , tattaunawa da zumunta a fagagen karantarwa
daban daban kan gida da makarantu da majami'u da masallatai. Ta
haka ne za mu iya kawar da tashin hankali tsakanin mabiya
addinai daban daban. Koyarwar shugabannin addinai tare da
litattafan makarantu wadanda ke gabatar da addinai ta
madaidiciyar hanya suna taimakawa sosai wajen tarbiyar yara
manyan gobe.
6 Fata na shi ne lura da wadannan batutuwan
da irin fuskantar da ta taso cikin al'ummar ku tare da abokan ku
Kirista za ta taimaka wajen ci gaba da tattaunawa da karuwar
mutuntawa da kwanciyar hankali wadanda a kan su na ke neman Albakacin
Allah
Jean-Louis Cardinal Tauran
Shugaba
Archbishop Pier Luigi Celata
Sakatare
|