The Holy See
back up
Search
riga

MAJALISAR PAPAROMA DA KE KULLA DA SAADAR
DA ZUMUNCI SAKANIN ADDINAI DABAM DABAM

Kirista da Musulumi:
Hada Hannu domin Darajar Iyali

SAKO NA MUSAMAN A KARSHEN WATAN RAMADAN

ID EL-FITIR 1429 H / 2008 A.D.

Abokaina Musulumi,

1. A yanzu da mun kusa ga karshen watan Ramadan, biye da alÂ’ada wadda ta riga ta kasance, Ina matukar farinciki in idar da gaisuwa ta musamman na majilisar Papa Roma da ke kulla da saÂ’adar da zumunci sakanin addinai a Vatican. A cikin wannan wata Kirista da ke tarayya da ku sun yi alÂ’ajibin tafsir da kuka saurara da kuma yin shagali tare da iyalanku; zancen zumunci da abokantaka sun kara kafuwa. Alhamdu lillahi!

2. Kamar yadda mun saba yi, lokaci kamar haka ya kan bamu zarafi domin mu yi tunani akan darasi masu yawa da zasu kawo mana cin gaba da kuma taimako a kokarin mu domin mu fahimcin juna da kyau, musamman ga inda muka bambanta da wadanda muka yarda tare. A wannan shekara muna bayar da shawara mu yi fadakarwa akan mutuncin iyali.

3. Daya daga cikin rebuce-rebucen Majalisar Vatican ta biyu watau Gaudium et Spes wadda ta yi magana akan Ikillisiya (Coci) a zamanin mu, ta ce: zaman kowanne dan Adam, da kuma na alÂ’ummar Kirista ya kasance da armashi, yana kuma hade da rayuwa lafiyar alÂ’umma wadda ta wurin ta ne ake yin aure a kuma sami iyali. Saboda haka ne Kirista da kuma sauran jamaÂ’a da ke darajanta alÂ’umma suke farinciki ta hanyoyi masu yawa da mutane ke samun taimako domin inganta wannan alÂ’umma ta kauna da cikakiyar rayuwa wadda ta wurin su ne iyaye ke samun taimako domin su awartar da kiran su. Daga bisani wadanda suke farincikin samun wannan taimako ne suke hangar kara moriyar su. (lambar 47)

4. Kalmomin nan masu gabata sun bamu zarafi mu tuna da cewa samun cingaba ta yan Adam da ta alÂ’umma sun dangana ne akan rayuwar iyali! A misali, Mutum nawa ne ke rayuwa, dauke da nauyin raunuka na azaba da asalin su daga iyalin da suka fitone? Maza da mata nawa ne ke rayuwa ta hanyan kwayoyi da hargisi ayau don neman su manta da wahalar rayuwar yarantaka amma basu samu ba? Mai yiwuwa ne, kuma wajibi ne Kirista da Musulumi su yi aiki tare domin sarafa daraja ta iyali, yau da gobe.

5. Bisa ga matsayi da fiko wadda Musulumi da Kirista sun ba wa iyali, mun sami lokatai masu dacewa, daga karkara har zuwa ga majalisar duniya inda muka yi aiki tare a wannan fanni. Iyali, wuri ne da mutane kan gogu cikin rayuwar kauna da bangirma da liyafa, a kuma koya yin wa wadansu. Shi yasa iyali shine tushin al'umma.

6. I, ya kamata Musulumi da Kirista su kasance suna taimakon iyalai da ke a cikin wahala. Amma bugu da kari, haki ne, su binciko su kuma yi aiki da wadanda suke goyon kokarin tabatar da karko da kuma zaman lafiya cikin iyalai, don iyaye su iya cin ma burinsu na koyas da iyalan su a hanyoyin da sun dace, a matsayin su na iyaye. Bari in tuna mana cewa Iyali shine farkon wurin da a ke koyan ladabi da biyayya da kuma bayar da girma ga kowa amma ba tare da mantawa cewa kowa yana da nasa halita wanda ta kasance dabam da na sauran mutane. Ta haka ne saÂ’adar da zumunci a cikin addinai da kuma kasa zasu ci ma burinsu.

7. YanÂ’uwna da kuma abokai, yanzu da lokacin azuminku ya kawo ga karshe, Ina fatan cewa ku da iyalan ku da duk wadanda ke kurkusa da ku, bayan tsarkakewa da sabuntuwar ta wannan alÂ’adar adininku mai muhumunci a gareku, zaku sami salama, kwanciyar rai da kuma arziki a rayuwar ku. Allah mai iko da girma ya cika ku da jinkai, da imani da kuma salama!

Jean-Louis Card. Tauran
Shugaba (President)

Pier Luigi Celata
Marubuci (Secretary)

 

PONTIFICAL COUNCIL FOR INTERRELIGIOUS DIALOGUE
00120 Vatican City
Phone : +39 06 698 84 321
Fax : +39 06 698 844 94
E-mail : dialogo@interrel.va

 

top