MAJALISAR PAPAROMA TA TATTAUNAWA TSAKANIN ADDINAI KIRISTA DA MUSULMI:
SAKON MASAMMAN A KARSHEN W AT AN RAMADAN ID-EL-FITR 1430H/2009 AD
Ya ku abokaina Musulmi 1. A cikin wannan lokacin idi da ke kawo karshen Azumin watan Ramadan, Ina so na mika fatan alheri na, na zaman lafiya da farin ciki gare ku, kuma da wannan sakon na. ba da shawara mu hada gwiwa kan manufar: Kirista da Musulmi Hada Gwiwa wajen kawar da talauci. 2. Wanan sakon na majalisar Tattaunawa Tsakanin Addinai ya zamo wata al' ada da duk muke kauna, da a kowace shekara ake saurare kuma ya zamo abin farin ciki. A shekaran nan ya zamo wani lokaci na sada zumunci a kasashe da yawa tsakanin Kirista da Musulmi. Sakon kan tabo wani batu da ya shafe mu duka, abinda yake karfafa juna wajen musayen ra'ayi. Ashe wannan bai ishe mu godewa Allah ba, a matsayin alama a fili ta abokantakar mu? 3. Idan muka komo kan taken mu na bana, za mu ga cewa, dan-adam na cikin halin fatara da rashi, abinda koyarwar addinan mu daban-daban ke motukar kiyayewa. Irin kulawa, da tausayi da taimako da mu iyan-uwa cikin zamanmu na yan-adam, za mu bayar wa talaka mu taimakesu su tsaya matsayin da ya dace cikin alumma, alama ce a fili ta kaunar Allah, don Shi ne ya umarce mu da nuna kauna da taimakon mutane ba tare da nuna wani bambanci ba. Kowa ya san yadda talauci ke iya jawo kaskanci da jurewa matsananciyar wahala. Shi ne ke jawo wariya, bacin rai, har ma da kiyayya da neman ramako. Yana iya jawo daukan mumunan mataki ta kowanne hali har ma da amfani da addini, ko kwace dukiyar mutum, gami da hana shi zaman lafiya cikin sunan ramakon Ubangiji. Wannan shi ya sa fuskantar ra'ayin rikau da tashin hankali cikin jama'a ya zamo mana dole, don mu magance matsalar talauci ta hanyar bunkasa rayuwar dan-adam kaman yadda Paparoma Paul VI ya bayyana shi a matsayin "Sabuwar Fuskar Zaman Lafiya" (Encyclical Letter Popolorum Progressio, 1975 n. 76). Cikin wasikarsa ta kwanan nan, Encyclical Letter Caritas in Veritate kan bunkasa rayuwar dan adam cikin bayaswa da gaskiya, Papo Benedict XVI yayi nuni da bukatar hadin kan jama'a (n4) bisa lura da kokarin da ake yi yanzu na raya al 'umma wanda ke nuna kara kasancewar dan adam na haliltar Allah, shi ya bashi matsayinsa na jigo ya zamo ga kowanne mutum, kuma ga kowanne bangaren rayuwarsa. (Populorum Progressio, n 42). 4. Cikin jawabinsa wajen bukin ranar Zaman Lafiya ta Duniya, ran I ga Janairu 2009, Mai Tsarki Paparoma Benedict XVI ya kasa talauci gida biyu: Talauci da za ayaka, da rashin da za a runguma. lrin talaucin da ya kamata a yaka a fili yake, Kaman yunwa, rashin ruwa mai tsafta, karancin kula da lafiya, da muhalli, da karancin kafofin ilimi da al'adu, ga jahilci, banda wassu sababbin fuskokin talauci. A manyan kasashe masu arziki, suma ana samun ambanci da rashin arziki na zuciya da na ruhaniyya (Message for the World Day of Peace, 2009, n: 2). lrin rashin da za a runguma shi ne na samun rayuwa mai sauki, mai gujewa barna da kulawa da muhalli, da kyawun halitta. Wannan zai iya hada wa da tsumulmula da azumi. Anan ne muke zaban abin da zai sa mu fadada zukatan mu, muna kallon bukatun wassu, ba na kanmu kadai ba. 5. A matsayin mu na masu imani, so muke yi mu yi aiki tare wajen samun kawar da talauci ta hanya mai dorewa da adalci. Abinda hakan ke nufi shi ne, yin tunani kan manyan matsalolin zamanin nan namu kuma inda duk dama ta samu, mu hada gwiwa wajen kawar da su. A nan maganarda ake yi kan talauci da danganta shi da dayantar duniya (globalization) tana da ma'ana ta fuskar da'a da ruhaniyya, domin duk mun amince da bukatar gina yan adam a matsayin iyali guda wanda kowa, mutane, da kasashe, za su tafiyar da kawunansu bisa manufofin yan-uwantaka dan kare hakki. 6. Nazarin yanayin talauci zai kai mu ga fahintar asalinsa na rashin mutunta dan adam da Allah ya hallice shi da ita, tare da kiran hada kan duniya, ga misali ta hanyar aiki da ka'idojin da muka amince da su, (John Paul II, Address to the Pontifical Academy of Social Sciences, 27 April 2001, n. 4) wadanda ba karbuwa kadai za su samu a duniya ba, har ma da kasarcewa masu tushe daga dokokin Allah a zukatan kowane dan adam (cf Rom, 14-15). 7. Akawai alama cewa a wurare daban-daban na duniya mun wuce jituwa zuwa haduwa tare, inda aka fara da musayar yanayin da ke danganta mu, da abubuwan da suke ainihin damun mu, wajen bayar wa kowa alherin rayuwar addua, azumi da sadaka da muke yiwa juna, ba zai yiwu tattaunawa tsakanin mu ta kai mu ga yin amfani da karfin masu fuskanta zuwa ga Allah? Tambayar matalauta garemu it ace suna kalubalen mu, amma fiye da komai suna kiran mu hada gwiwa cikin wannan aikin alheri; kawar da talauci!
Jean-Louis Cardinal Tauran
Archbishop Pier Luigi Celata
PONTIFICAL COUNCIL
|
|