The Holy See
back up
Search
riga

MAJALISAR PAPAROMA
TA TATTAUNAWA TSAKANIN MABIYA ADDINAI

SAKON KAMMALA AZUMIN WATAN RAMADAN
Id al-fitir 1433AH/2012 AD

ILMANTAR DA MATASAN KIRISTADA NA MUSULMI
A KAN GASKIYA DA ZAMAN LAFIYA

 

Ya ku abokanaina Musulmai,

Wannan bukin murnar karamar Sallah wanda ke zuwa bayan kamala azumin watan Ramadan ya baiwa majalisar koli na Paparoma kan samun fahimta tsakanin addinai na mika muku dumbin gaisuwa.

Muna ma su farin ciki da Allah ya nuna mana wannan lokaci, inda ku ka samu dammar kara himma wajen bautar Ubangiji ta hanyar yin azumi da kuma yin wasu aiyukan bauta da mu ma ka mu muka yi imani da su.

Wannan shi ya sa muka ga ya kamata a wannan shekaran mu duka mu sa himma wajen ilmantar da matasan Krista da na musulmai a kan adalci da zaman lafiya wandan ba sa taba rabuwa da gaskiya da kuma yanci.

2. In hakkin ilimi abu ne da ya rataya kacokam kan kasa, to, kamar yadda ku ka sani, hakkin iyaye na gaba kafin mu yi maganar iyalai da makarantu da kuma jami’o’i, ban kuma manta da sauran hakkoki na rayuwar addini da al’ada, jin dadi da tattali da kuma muamullan duniya ba. Cimma wadannan, abubuwa ne ma su kyau, amma kuma abu ne mai wuya, ka tallafa wa yara da matasa su gano sannan su gina kan irin baiwan da Allah Madaukaki ya yi mu su, ta hanyar inganta muamullan zamantakewa. In zan koma baya kan hakkin masu ilmantarwa, Mai Tsarki Paparoma Benedict XVI kwanannan ya ce; “A sabili da haka, yau ne fa muka fi bukatan shedun gaskiya, amma ba irin mutanen da za su zauna su ce an ce ba…. Shedan da ake magana shi ne mutumin da yake kan tafarkin da yake so saura su bi”. (“Sakon Ranar Zaman Lafiya na Duniya” 2012) Bayan haka, mu fa sani, su ma matasan na da hakkin ilmantar da kawunansu da kuma tsayawa ta farkin gaskiya da zaman lafiya.

3. Gaskiya na tabbata ne a farko daga ayyukan mutum cikin rayuwar sa ko rayuwar ta, domin kuma ba abu ne na zabi ko kuma wanda za’a iya raba shi ba. Ka da fa mu manta cewar ba za a taba cimma kauna ba in ba bu hadin kai da kuma soyayyar zuci. Ga ma su ban gaskiya, kwatanta gaskiya da kusantan Allah na karfafa sauran muamulla da kai kan ka da sauran alamuna da kuma duk wani abin da Allah ya halitta. Bugu da kari an yi hasashen cewar gaskiya na da tushen ta, sanin kowa ne cewar Allah ne ya yi duk mutane kuma ya umuce su da su zama iyali daya. Irin wannan hangen nesan mai cike da tunani, ba abu ne da za mu yi tantama ba, illa ya umurci dukkan maza da mata ma su aniya ta gari da su hada kai cikin duk abubuwan da za su yi.

4. A wannnan zamanin da muka samu kanmu, ya zama wajibu mu ilmantar da matasan mu kan zama lafiya. Idan za mu sauke nauyin dake kanmu, wajibi ne mu san menene zaman lafiya wanda bai tsaya kan rashin yaki ko kuma cimma matsaya tsakanin juna ba, amma kyauta ce daga Allah da kuma kokarin dan Alan ya bi shi ba kakkautawa. Daga karshe za a samu gaskiya da kuma taimakakkeniya. Ya na da muhimmanci mabiya su tashi tsaye da yin aiki tukuru a duk inda suka samu kansu ta hanyar nuna kansu ta hanyar nuna tausayi da yan-uwartaka da hadin kai da kuma kauna.

Wadannan za su taimaka wajen magance kalubalen da muke fuskanta a yau na zaman tare da cin gaban kasa da kiyayewa da kuma magance duk wani abin da zai tada hankali da dai sauran su.

5. Daga karshe, ina yin kira kan matasan musulmi da na Krista wadan da Allah zai basu ikon karanta wannan sako na, dasu kasance ma su gaskiya da walwala domin su kasance jakadun gaskiya wajen gina sanin yakamata, da zaman lafiya da kuma mutunta yancin kowa. Muna yin kira a garesu dasu ringa hakuri da kuma kai hankali nesa wanda ta haka ne za a iya cimma wadannan kudurori a maimakon rudi da yaudara ko kuma rashin nuna imani ga dan adam. Sai mutane maza da mata da suka amince a cikin kahon zuciyanssu kan wadannan batutuwa ne za su iya bada gudummawa wa zamantakewan alumma a inda gaskiya da zaman lafiya zai kasance a zahirance.

Ga iyalai da kuma sauran jama’an dake da burin son zama jakadun wanzar da zaman lafiya, muna rokon Allah da ya cika zukatansu da hakuri da kuma imani.

Ina yi muku duka fatan a yi bukukuwa lafiya.

Daga Vatican, 3, Agusta 2012

Jean–Louis Cardinal Tauran
President

Archbishop Pier Luigi Celata
Secretary

 

 

MAJAKISAR PAPAROMA
NA SAMUN DAIDAITAUWA DA SAURAN ADDANAI
00120 BIRNI VATICAN

Telephone: 0039-06-6988 4321 / 06-6988 3648
Facsimile: 0039-06-6988 4494
Email: dialogo@interrel.va

    

top